Essien ya koma horo tare da Ghana

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Micheal Essien

Dan kwallon Ghana, Micheal Essien ya koma horo da karfinsa a yayinda kasar ke shirin haduwa da Jamus a gasar cin kofin duniya.

Dan wasan mai shekaru 31 ya ji raunin a dan yatsarsa a karawar da suka sha kashi a daci biyu da daya a hannun Amurka.

Essien sai a ranar Alhamis ya koma horo bayan hutun.

An caccaki kocin Black Stars, Kwesi Appiah saboda barin Essien da Kevin-Prince Boateng a benci a wasan da Amurka ta doke su.

Karin bayani