Ba zamu kori Hodgson ba - Dyke

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Roy Hodgson na fuskantar matsin lamba

Shugaban hukumar kwallon Ingila, Greg Dyke ya ce Roy Hodgson zai ci gaba da kasancewa a matsayin kocin Ingila har zuwa shekara ta 2016.

Ingila ba za ta kai zagaye na biyu ba a gasar cin kofin duniya saboda ta sha kashi a wasanninta biyu a jere.

Dyke ya ce "Muna goyon bayan Roy, tabbas zai ci gaba da jan ragama."

An nada Hodgson a shekara ta 2012 bayan da Fabio Capello ya ajiye mukaminsa.

Tuni tsohon kyaftin din Ingila, Alan Shearer ya bayyana goyon bayansa ga Hodgson ya ci gaba da jagorantar tawagar 'yan kwallon Ingila.

Karin bayani