Kenya ta yi gargadi kan kallo cikin jama'a

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fiye da mutane 60 ne suka mutu a harin bama-baman da aka kai Mpeketoni

Gwamnatin Kenya ta bukaci 'yan kasarta da su kalli gasar cin kofin duniya a gidajensu, maimakon wuraren da jama'a ke taruwa.

Hakan ya biyo bayan harin da aka kai a yankin da ke gabar teku a farkon makon nan.

Ma'aikatar cikin gida ta kasar ta kuma nemi masu wuraren sayar da barasa da gidajen abinci su dauki matakan kariya.

Tana mai cewa masu aikata laifi za su iya amfani da lokacin kallon gasar cin kofin duniyar, domin aikata miyagun ayyuka.