Ronaldo ya koma horo da Portugal

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cristiano Ronaldo a horo

Cristiano Ronaldo ya koma horo tare da tawagar Portugal bayan da aka nuna fargaba cewar ba zai kara buga gasar bana ba.

Dan wasan Real Madrid mai shekaru 29, na fama da rauni a idon sawunsa amma kuma ya yi 'yar sassarfa a ranar Juma'a.

A ranar Laraba ne gwarzon dan kwallon duniya, Ronaldo ya fita daga cikin horo yana din gishi, inda aka daura masa kankara a kafarsa.

Portugal na rukunin D, kuma wasanta na farko ta sha kashi a wajen Jamus da ci hudu da nema, kuma a ranar Lahadi za ta hadu da Amurka.

Karin bayani