Kanin Yaya da Kolo Toure ya rasu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yaya na Brazil aka sanarda shi rasuwar kaninsa

Kanin 'yan kwallon Ivory Coast Yaya da Kolo Toure ya rasu a daidai lokacin da suka halartar gasar cin kofin duniya a Brazil.

Ibrahim Toure mai shekaru 28 ya rasu a ranar Alhamis a birnin Manchester.

Hukumar kwallon Ivory Coast ta ce "Tawagar Ivory Coast gaba dayanta na taya su jimamin wannan rashin".

Ibrahim Toure wanda dan kwallo ne, a baya ya taka leda a kungiyar Al-Safa SC a kasar Lebanese.

A bayyanawa Yaya da Kolo rasuwar kaninsu ne sa'o'i kadan bayan kasar ta sha kashi a hannun Colombia da ci biyu da daya.

Karin bayani