Argentina ta doke Iran 1-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Messi ya jaddada matsayinsa na fitaccen dan kwallo

Kwallon da Lionel Messi ya zira a karin lokaci ta baiwa Argentina damar doke Iran da ci 1-0 a Belo Horizonte, abinda ya basu damar kaiwa ga zagaye na biyu.

Iran sun musguna wa Argentina - wacce ta lashe kofin duniya sau biyu a tsawon lokaci, yayin da Alireza Haghighi ya hana Sergio Aguero zira kwallo.

Suma Iran sun samu damar lashe wasan ta hannun Ashkan Dejagah amma Sergio Romero ya hana shi.

Sai dai Messi ya fitar da Argentina kunya da kwallon da ya zira a mintinan karshe.

Karin bayani