Ghana ta yi canjaras 2 -2 da Jamus

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Ghana ta yi canjaras 2 -2 da Jamus a rukunin G na gasar cin kofin duniya a Brazil. Götze (51') A.Ayew (54') Klose (71') Gyan (63')

Mun kawo karshen wannan sharhi kai tsaye, muna godiya ga dukkan wadanda suka shigo wannan shafi. Sai a kasance da mu a rediyo idan an jima da misalin karfe 10.30 domin sharhi kan wasan Nigeria da Bosnia-Herzegovina.

Sharhi: Ghana sun farfado da kimar Afrika a wannan wasan, saura Super Eagles na Nigeria, a cewar wakilin BBC Farayi Mungazi

Duka bangarorin biyu sun taka leda sai dai Jamus za su yi farin ciki da sakamakon ganin cewa su ne suka farke daga karshe. Su ma Ghana akalla sun taka rawar gani ganin cewa sun sha kaye a wasansu na farko.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An tashi wasa Jamus 2-2 Ghana
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sully Muntari Ghana - ba zai buga wasan gaba ba

Ra'ayoyin daga shafinmu na BBC Hausa Facebook

Atiku DanYarbawa Barbarejo "Yanzu haka, kowa sai murna yake yi a nan Accra Ghana, tare da bushe-bushe da guje-gujen ababen hawa, saboda yadda Black Stars suke murza leda".

Isah'easy Jumbam "Mu dai munanan a bayan ku Ghana, Up Up Up Afrika".

Isah Ibrahim "Haha ana dara ga dare ya yi Up Ghana."

Mintina 91: Ghana sun samu dama mutum uku da biyu amma Wakaso ya yi satar gida.

Mintina 90: An kara minti uku. Jamus sun samu kwana.

Mintina 89: Jamus sun kai mummunar kora ta hannun Miroslav Klose amma ya buga kwallon waje.

Mintina 88: Ghana sun sake kai kora amma wannan karon Gyan ya buga kwallon waje.

Mintina 87: Ghana sun sake kai kora ta hannun Jordan Ayew amma Neuer ya cafke kwallon ba tare da matsala ba.

Mintina 83: Ghana sun kai kora inda Gyan ya barar da kwallon da ka. Daga nan kuma sai Jamus suka fisga inda suka sake kai mummunar kora tare da samun kwana. Amma dai Ghana sun cire kwallon ba matsala.

Mintuna 80: Idan aka tashi wasa biyu da biyu, Jamus ta fi Ghana damar kaiwa zagaye na biyu saboda a wasan Ghana na farko, Amurka ta doke Black Stars din.

Sharhi: Dan kwallon Jamus, Miroslav Klose ya zura kwallaye 15 kenan a gasar cin kofin duniya. A yanzu ya kamo Ronaldo De Lima na Brazil wanda a baya ya kafa tarihin dan kwallon da yafi kowanne cin kwallaye a gasar cin kofin duniya.

Mintina 77: Ghana sun samu kwana ta hannun Mubarak Wakaso. Sai dai Jamus sun fitar da kwallon ba tare da wata matsala.

Ra'ayoyi daga BBC Hausa Facebook:

Hamza Ahmad Jinjiri ya ce "Ghana Allah ya bada sa'a".

Yasir Iliyas Sulaiman ya ce "Up Black Stars".

Mintuna 75: Jamus 2 Ghana 2 Götze (51') A.Ayew (54') Klose (71') Gyan (63')

Hakkin mallakar hoto AP
Hakkin mallakar hoto AFP
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ghana: Mubarak Wakaso ya karbi Christian Atsu.
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mintina 70: Jamus 2-2 Ghana Miroslav Klose. Daga kwana ya taba ta da kafa da taimakon Benedikt Höwedes
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jamus: Bastian Schweinsteiger ya karbi Sami Khedira.
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jamus - Miroslav Klose ya karbi Mario Gotze

Mintina 66: Jordan Ayew ya kai kora mai kyau amma ya buga kwallon ga Neuer kai tsaye. Wannan ba karamar dama bace ga Ghana ta suka kara kwallo.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jamus 1-2 Ghana Asamoah Gyan. Kwallo da kafar dama tare da taimakon Sulley Ali Muntari

Mintina 60: Jamus sun kai kora ta hannun Mustafi amma mai tsaron gidan Ghana ya kama kallon ba tare da matsala ba.

Mintina 57: Ghana sun samu bugun tazara a kusa da gidan Jamus amma Muntari ya buga ta waje.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mintina 54: Jamus 1-1 Ghana Andrew Ayew da ka tare da taimakon Harrison Afful
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mintuna 50: Jamus 1-0 Ghana. Mario Gotze kwallo ya narka da hagu tare da taimakon Thomas Müller

Mintina 48: Toni Kroos ya samu bugun tazara.

An dawo zagaye na biyu Ghana 0-0 Jamus

Idan an jima kadan Nigeria za ta kara da Bosnia. Za mu kawo muku sharhi kai tsaye a rediyo tare da Aminu Abdulkadir da Aliyu Tanko da kuma Naziru Mika'ilu - sai a kasance tare da mu daga karfe 10.30 agogon Nigeria.

Ra'ayoyi a BBC Hausa Facebook

Usman A Shuraihu ya ce " Allah ya ba mai rabo sa'a"

Ali Jiniya Gumel ya ce "Kunayi muna jin dadi, Up Ghana"

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasa ya kai wasa kusan za a iya cewa duka bangarorin biyu sun taka rawar gani
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ghana 0-0 Jamus

Mintina 44: Ghana sun kai kora inda suka samu kwana. Muntari ya bugu kwallon, Neuer ya fito amma bai same ta ba, sai dai ta yi gefe ba tare da matsala ba.

Za ku iya bayyana ra'ayoyinku kan wasan ta shafukanmu na BBC Hausa Facebook ko ta Twitter.

Mitina 40: Muller ya kai kora inda ya bugu kwallo a gidan Ghana amma babu kowa a cikin 'yan wasan Jamus.

Mintuna 40: Ghana 0-0 Jamus

Hakkin mallakar hoto AP

Ghana na kai hare-hare masu hadari musamman a bangaren hagu inda Andre Ayew ke buga kwallo. Ayew dan tsohon gwarzon dan wasan Afrika ne Abedi Pele.

Mintina 36: Gotze ya kai hari da taimakon Khedira amma mai tsaron gidan Ghana ya kama.

Mintina 33: Gyan ya ja kwallo a gidan Jamus amma Neuer ya fito - kwallo ta fita ba matsala ga Jamus.

Mintina 32: Sulley Muntari ya kai mummunan hari da karfi inda Neuer ya kade ta da kyar.

Mintuna 30: Ghana 0-0 Jamus

Mintina 29: Jamus sun kai kora ta hannun Muller amma ta fita kwana bayan da dan bayan Jamus ya ture ta.

Mintina 26: Gyan ya yi satar gida, bugun tazara ga Jamus.

Mintina 25: Kurus ya kai kora amma kwallon ta yi sama

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption 'Yan gida daya suna gaisawa Boateng da Boateng

Mintina 21: Jamus sun kai kora amma Muller bai samu yadda yake so ba.

Mintina 18: Khedira (Jamus) ya kai kora amma mai tsaron gidan Ghana ya kame kwallon ba tare da mtsala ba.

"Christian Atsu nedan wasan da ya fi kowanne taka rawar gani a wasan Ghana na farko" a cewar mai yiwa BBC sharhi kuam tsohon dan wasan Ingila Danny Murphy.

Mintuna 15: Ghana 0 -0 Jamus

Mintina 12: Ghana ta kai harin cin kwallo amma kuma sai golan Jamus, Neuer ya kabe kwallon.

Mintina 11: Jamus suna kai kora saura kiris bayan da Mouler da Ozil suka tattaba suka baiwa Kurus amma yan bayan Ghana sun tare.

Mintina 9: Ghana ta samu bugun tazara, bayan da Khedira ya fadar da Kwadoh Asamoah

Mintina 6: Ghana sun fara wasan da kyau - Christian Atsu ya taimakawa Gyan ya kai hari mai kyau

Hakkin mallakar hoto AFP

Mintina 2: Sulley Muntari (Ghana) ya samu bugun tazara.

Ra'ayoyi daga BBC Hausa Facebook

Aminu Dankaduna Amanawa ya ce "Gaba Dai Gaba dai kasar Jamus muna bayanku, a wasan da za ku buga da kasar Ghana".

Ibrahim Yusuf Abdullahi ya ce "Muna tare daku daya daga cikin wakilan Afrika watau Ghana".

0:00 An fara wasa Ghana 0-0 Germany

19:59 A wasan da Ghana da buga na farko, Amurka ta doke ta da ci biyu da daya. Ita kuma Jamus a wasanta na farko ta lallasa Portugal da ci hudu da nema

19:57 Kocin Ghana, Kwesi Appiah ya ziyarci filin wasan Liverpool a kakar wasan da ta wuce domin kara gane kamun ludayin yadda ake horadda 'yan kwallo.

19:56 'Yan wasa sun fito fili ana taken kasashen biyu inda aka fara da na Jamus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan uwan juna Boateng da Boateng za su fafata da juna
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Filin wasa ya dau harami - magoya bayan Jamus sun dau kwalliya suna jiran a fara taka leda.

19:50 To muna dai sanar da masu saurarenmu cewa suna iya jin sharhi da bayanai kai tsaye ta rediyo na wasan da za'a yi tsakanin Najeriya da Bosnia-Herzegovina a kan mita 25 da kiloHerzt 12080. Za mu fara sharhin ne daga karfe goma da rabi na yamma agogon Nigeria.

Hakkin mallakar hoto Getty

19:46 Tun da farko Argentina ta doke Iran da ci 1-0 bayan da Lionel Messi ya zira kwallon ana dab da tashi.

19:39 Za ku iya bayyana ra'ayoyinku kan wasan ta shafukanmu na BBC Hausa Facebook ko ta Twitter.

19:37: 'Yan wasan Jamus: Neuer, Howedes, Hummels, Khedira, Ozil, Muller, Lahm (c), Mertesacker, Kroos, Gotze, Boateng.

19:33 'Yan wasan Ghana: Dauda, Gyan (c), Atsu, Boateng, A Ayew, Muntari, Rabiu, Mensah, Asamoah, Boye, Afful.