Kofin Duniya: Belgium ta doke Rasha 1-0

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Eden Hazard ne ya bugo kwallon da Origin ya samu ya ci

Kasar Belgium ta shiga zagaye na biyu na 'yan 16 na gasar cin kofin duniya bayan da ta ci Rasha 1-0 ana saura minti biyu lokaci ya cika.

Divock Origi ne da ya shigo daga baya ya ci wa Belgium din kwallon wadda ita ce kwallon farko da ya taba ci wa kasar.

Belgium ita ce ta daya a rukuninsu na takwas wato Group H da maki shida a wasanni biyu Rasha ita ma da wasanni biyu tana da maki daya a matsayin ta uku.

Korea ta Kudu wadda ta yi wasa daya tana da maki daya a matsayin ta biyu, yayin da Algeria take matsayin ta karshe a rukunin da wasa daya ba maki.