Joachim: Klose kyakkyawan zabi ne

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ronaldo ya ce, ''na san yadda yake jin dadi da ya yi wannan bajinta, ina masa maraba da shigowa tawagar.''

Kocin Jamus Joachim Low ya ce sanya Miroslav Klose a tawagar 'yan wasan Jamus muhimmin abu ne, bayan da dan wasan ya kai bajintar Ronaldo ta cin kwallaye 15 a gasar kofin duniya.

Dan wasan ya ceci Jamus da ya rama musu kwallo ta biyu da suka yi canjaras 2-2 da Ghana da taba kwallonsa ta farko minti biyu da sa shi wasan.

Bayan kamo Ronaldo tarihi, da kwallon da ya ci Ghanan, ya kuma zama dan wasa na uku da ya ci kwallo a gasar kofin duniya hudu bayan Uwe Seeler shi ma dan Jamus da Pele na Brazil.

Kocin ya ce, '' na yi matukar farin ciki da Klose, mintinsa biyu da shiga fili kuma ya ci kwallo.''

''Abin alfahari ne gare ni ya kasance ina da dan wasa irin Klose a ajiye, da sanin cewa zai iya sauya al'amari.''

Klose mai shekara 36 wanda ya fara buga wa Jamus wasa a watan Maris na 2001 yanzu ya fi kowa yawan ci wa kasar kwallo inda yake da 70.

Ya wuce Gerd Muller mai kwallo 68, kuma kwallon da ya rama a wasan Ghana ta sa ya zarta Muller a yawan kwallayen da suka ci a kofin duniya da kwallo daya.