''Fitar Ingila ba abin kunya ba ne''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho ya ce, ''Ingila ta yi kokari a wasanninta ba ta ji tsoron Uruguay ba,, ba ta ji tsoron Italiya ba.''

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce ba abin kunya ba ne fitar da Ingila da wuri daga gasar cin kofin duniya a Brazil.

Rashin nasarar da Ingila ta yi a wasanta da Italiya da Uruguay ya hana ta wucewa gaba da matakin rukuni a karon farko tun 1958.

Mourinho mai shekara 51 ya ce idan ya soki Ingila kan kasawarta a gasar da ake yi a Brazil bai yi mata adalci ba, saboda ba wani abin kunya ta yi ba.

Ya ce ba suda sa'a ne kawai, domin a cewarsa tun lokacin da aka yadda kasashe za su fafata a gasar, a bara aka saka Ingilan cikin rukuni mai tsanani.

Ranar Talata ne Ingila za ta yi wasanta na karshe na rukuni na hudu , Group D da Costa Rica da ta kai zagaye na biyu