Ghana ta musanta cogen wasanni

Shugaban hukumar kwallon Ghana, Kwesi Nyantakyi
Image caption Fifa ta ce lamarin ba zai shafi martabar gasar cin kofin duniya ba

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Ghana ya musanta cewa hukumar ta amince tawagar 'yan wasan kasar su yi wasannin da aka yi cogensu.

Hukumar ta kuma yi kira ga 'yan sanda su gudanar da bincike a kan zargin.

Zargin ya biyo bayan wani binciken karkashin kasa ne da wani gadan talabijin na Channel 4 da kuma jaridar Daily Telegraph suka yi.

Shugaban hukumar kwallon, Kwesi Nyantakyi, ya shaida wa BBC cewa "Babu gaskiya a abin da suka wallafa."

Masu binciken dai sun gano mutane biyu, daya wakili ne na hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, dayan kuma wani jami'in wata kungiyar kwallon kafa a Ghana ne, kuma mutanen biyu sun ce za su iya cogen wasannin sa da zumunta da Ghana za ta buga.