Coge: Ghana za ta kai karar Telegraph

Kwesi Nyantakyi
Image caption Hukumar GFA ta musanta hannu a cikin lamarin

Shugaban Hukumar kula da kwallon kafa ta Ghana Kwesi Nyantakyi zai kai karar jaridar Daily Telegraph ta Burtaniya bayan da ta yi zargin cewa ya amince kasar ta buga wasannin da aka yi cogensu.

Zargin ya zo ne bayan binciken hadin gwiwa tsakanin jaridar da kuma shirin gidan talabijin na Channel 4 Dispatches.

Nyantakyi ya shaida wa BBC cewa "bayanan da aka wallafa a rahoton ba gaskiya ba ne".

Hukamar ta GFA ta kuma yi kira ga 'yan sanda da su binciki zarge-zargen.

Karin bayani