Man United za ta sayi Herrera

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ander Herrera

Manchester United na gab da sayen dan kwallon tsakiya na Athletic Bilbao Ander Herrera wanda ake ganin zai kai fan miliyan talatin.

Dan kwallon Spain din mai shekaru 24, ana saran cikin sa'o'i 24 za a kamalla yarjejeniya da shi.

Idan har cinikin ya kullu, zai kasance dan kwallo na farko da sabon kocin United, Louis van Gaal ya saya.

Herrara na cikin tawagar Spain a gasar Olympics a London a shekara ta 2012.

Tun bayan da ta sayi Marouane Fellaini daga Everton a kakar wasan da ta wuce, United ba ta kara sayen dan kwallon tsakiya ba.

Karin bayani