Netherlands ta doke Chile 2-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Netherlands ce ta zamo ta daya a rukunin na B

Netherlands ta zamo ta daya a rukunin B a gasar cin kofin duniya bayan da Leroy Fer da Memphis Depay suka zira kwallaye biyu a wasan da suka doke Chile da ci 2-0 a Sao Paulo.

Duka bangarorin biyu sun ringa sun tsallake zuwa zagaye na biyu bayan da suka lashe wasanninsu da Spain da Australia.

Fer headed - wanda ke taka leda a Norwich City a minti na 77, kafin Depay ya zira ta biyu a minti na karshe.

A yanzu mai yiwuwa Chile ta kara da Brazil a zagaye na biyu, yayin da ake sa ran 'yan wasan na Louis Van Gaal suka kara da Mexico ko Croatia.

Karin bayani