Keshi ya yi wa Okocha raddi

Image caption Keshi ne ya jagoranci Nigeria ta lashe gasar kofin Afrika

Kocin Nigeria, Stephen Keshi ya maida wa tsohon kyaftin din Super Eagles Jay-Jay Okocha martani game da salon wasansa a gasar cin kofin duniya.

Bayan wasan Nigeria na farko tsakaninta da Iran inda aka tashi babu ci, sai Okocha ya caccaki salon wasan kasar.

Keshi ya ce "Mutane na da 'yancin rike ra'ayinsu amma kuma wasu sun cika son bata mutane".

Nigeria na da damar tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar inda har ba ta sha kashi a wajen Argentina ba.

A waje daya kuma hukumar kwallon Afrika ta Kudu ta musanta jita-jitar cewa Stephen Keshi ne zai zama sabon kocin Bafana Bafana.

Karin bayani