Kofin Duniya: Lampard zai zama kyaftin

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lampard shi ne dan wasan Ingila na takwas da ya kai bajintar buga mata wasanni 100.

Frank Lampard zai rike kyaftin din Ingila a wasansu na karshe na gasar kofin duniya da Costa Rica, wanda ake ganin shi ne wasansa na karshe na Ingila saboda Steven Gerrard zai huta a wasan.

Lampard mai shekara 36 wanda ya shirya barin Chelsea ana ganin ba zai sake buga wa Ingila wasa ba bayan wasan nata na ranar Talata.

Daman Lampard ya rike mukamin na kyaftin a wasan da Ingila ta yi na sada zumunta da Ecuador ranar hudu ga watan Yuni.

Lampard shi ne dan wasan Ingila na takwas da ya kai bajintar buga mata wasanni 100 lokacin wasanta da Ukraine a watan Satumba na bara.

Dan wasan da ya buga manyan gasanni biyar, da suka hada da gasar kofin duniya ta yanzu, ya zama dan wasa na tara da suka fi ciwa Ingila kwallo a tarihi har guda 29.

Shi ma Steven Gerrard na tunanin makomarsa bayan fitar da Ingila a gasar ta kofin duniya a matakin wasannin rukuni.