Murray ya fara kare Wimbledon da sa'a

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Murray ya ce, ''da farko na yi tsammanin wasan mai wahala ne''

Andy Murray ya fara kare kambunsa na gasar tennis ta Wimbledon da sa'a inda ya doke David Goffin da ci 6-1 6-4 7-5.

Goffin dan Belgium shi ne na 105 a jerin gwanayen tennis na duniya.

Murray mai shekaru 27 na uku a gwanayen tennis a duniya zai kara da Blaz Rola dan Slovania a zagaye na biyu ranar Laraba.

Dan wasan shi ne dan Birtania na farko da zai kare kambun na Wimbledon tun Fred Perry da ya dauki kofin karo na uku a 1936