Portugal da USA sun tashi 2-2

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ronaldo ya taimaka wajen cin kwallo ta biyu inda wasan ya tashi 2-2

A ci gaba da gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a kasar Brazil, an fafata tsakanin Portugal da USA inda suka ta shi ci 2-2.

USA na kan gaba da ci biyu Kasar Portugal na da daya inda magoya bayan USA ke ta murna ganin ga lokaci ya kusa cika.

Ashe dai murna zata koma ciki, ana dab da hura tashi, dan wasan Portugal Varela ya kara ta biyu inda ya ci kwallon da ka ta hanyar yin sufa.

Wannan kunnen doki tsakanin Jamus da USA gaba ta kai su a rukunin Group G, yayin da Portugal ya zame mata wajibi ta ci Ghana in har ta na son tsallakewa zuwa wasan gaba.