Spain ta lallasa Australia da ci 3-0

Spain ta lallasa Australia da ci 3-0 Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An fitar da duka Spain da Australia daga gasar

Masu rike da kanbun gasar cin kofin duniya Spain sun yi bankwana da gasar tare da doke Australia da ci 3-0 a rukunin B a Curitiba.

Kwallaye daga David Villa, Fernando Torres da Juan Mata sun kare Spain daga shan kashi sau uku a jere a karon farko tun shekara ta 1991.

Villa ne ya fara zira kwallo tare da taimakon Juanfran, kafin dan wasan Chelsea Torres ya zira ta biyu.

Juan Mata da ya shigo daga baya ya zira ta uku tare da taimakon Cesc Fabregas wanda shi ma ya shiga wasan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Karin bayani