Van Gaal ya zargi Fifa da fifita Brazil

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sai dai kocin Brazil Scolari, ya ce, ba wai suna zaben kasar da za su kara da ita ba ne, Fifa ce ke tsara lokacin kowanne wasa.

Kocin Holland Louis van Gaal ya zargi Fifa da shirya kumbiya-kumbiya a jadawalin wasannin kofin duniya domin fifita Brazil.

Brazil mai masaukin baki ta yi wasa kafin Holland a wasanni biyu na farko amma kuma a wasan karshe na rukuni-rukunin sai Holand ta yi wasa sannan Brazil ta yi, wanda hakan zai sa Brazil ta san kasar da za ta hadu da ita.

Louis van Gaal wanda kungiyarsa za ta iya haduwa da Brazil ya ce hakan rashin adalci ne.

Jadawalin Wasannin

Duk kasar da ta zama ta daya a rukunin farko wato Group A na Brazil, za ta hadu da ta biyun rukuni na biyu wato Group B , ranar Asabar, yayin da ta biyu a Group A za ta hadu da ta farko a B ranar Lahadi.

Brazil ce ke jagorantar Group A kuma tana bukatar canjaras da Kamaru, wadda tuni ta yi waje bayan da Crotia da Mexico suka ci ta.

Idan Brazil ta yi nasara a wasanta na Litinin da Kamaru (karfe tara na dare agogon Nigeria), za ta zama ta daya, idan suka yi canjaras ko rashin nasara matsayinsu zai dogara ga sakamakon wasan Crotia da Mexico wadanda za su yi wasan a lokaci daya.

Crotia tana bukatar nasara yayin da Mexico ke bukatar akalla canjaras ta tsallake.

Shi kuwa wasan Group B da za a yi da karfe biyar na yamma (agogon Nigeria), Holland da Chile tuni sun tsallake, amma Holland na bukatar canjaras ne kawai ta zama ta daya, abin da van Gaal yake so domin kauce wa Brazil.

Karin bayani