''Ba sabon abu ba ne kin yi wa Ingila wasa''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Taylor wanda ya yi kocin Ingila tsakanin 1990 zuwa 1993 ya ce, wasan kungiya na shan gaban na kasa.

Tsohon kocin Ingila Graham Taylor ya ce ba wani sabon abu ba ne, 'yan wasa su ki yi wa kasarsu wasa.

Kocin na mayar da martani ne kan maganar da kocin QPR Harry Redknapp ya yi, cewa a lokacin yana Tottenham ya yi fama da 'yan wasan da ke kokarin kin zuwa wasan Ingila.

Taylor ya ce a wasu lokutan masu horad da kungiyoyi ne ke dora wa 'yan wasan nauyin da yake sa su ki halartar wasannin kasarsu.

Shi kuwa kyaftin din Ingila Steven Gerrad ya bukaci Redknapp ne ya bayyana sunayen 'yan wasan da suka ki amsa gayyatar Ingilan.

Redknapp wanda ya yi kocin Tottenham tsakanin 2008 da 2012, yana bayyana ra'ayinsa ne kan ficewar Ingila daga gasar kofin duniya da ake yi, bayan wasanni biyu na rukuni kawai.