Uruguay ta doke Italiya da ci 1-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan Uruguay na murnar nasarar

Uruguay ta tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya bayan ta samu galaba a kan Italiya da ci daya mai ban haushi.

Diego Godin ne ya ci wa Uruguay kwallo bayan da aka baiwa dan kwallon Italiya Claudio Marchisio jan kati ana sauran minti 30 a tashi wasa.

Sai dai wasan ya bar baya da kura, bayan da dan kwallon Uruguay Luis Suarez ya ciji dan wasan Italiya.

Kenan an fitar da Italiya a wannan gasar saboda maki uku kadai ta samu daga wasanni uku.

A shekara ta 2010, an fitar da Italiya a zagayen farko na gasar cin kofin duniya.

Karin bayani