Luis Suarez ya kara yin cizo

Image caption Karo na uku ke nan Suarez yana cizo a wasa

Dan kwallon Uruguay Luis Suarez ya kara jefa kansa cikin cece-kuce bayan da ya gantsarawa dan kwallon Italiya Giorgio Chiellini cizo a kafada.

Hakan ya sa Chiellini ya ja rigarsa ya nuna wa alkalin wasa inda alamun cizon yake a kafadarsa.

A cikin watan Afrilun 2013, aka dakatar da Luis Suarez na Liverpool daga buga wasanni 10 saboda cizon dan wasan Chelsea Branislav Ivanovic.

A shekara ta 2010 ma, an dakatar da Suarez na wasanni bakwai saboda cizon dan wasan PSV Eindhoven Otman Bakkal lokacin Suarez din yana kyaftin din Ajax.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chiellini yana nuna inda Suarez ya cije shi

Karin bayani