Bosnia ta doke Iran da ci 3-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bosnia ta lashe wasa a karon farko a wata babbar gasa

Fatan Iran na kaiwa zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya bayan da ta sha kashi a hannun Bosnia-Hercegovina da ci 3-1.

Tawagar ta Carlos Queiroz sun fara wasan da damar tsallake wa, sai dai kwallon da Edin Dzeko ya zira ta kashe musu gwiwa.

Dan wasan Roma Miralem Pjanic ne ya zira ta biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Reza Ghoochannejad ya zira wa Iran kwallonta daya tilo a gasar, sai dai Avdija Vrsajevic ya zira ta uku domin baiwa Bosnia damar lashe wasa a karon farko a tarihinta.

Karin bayani