Ghana ta tura $3m ga 'yan kwallonta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ghana na bukatar lashe Portugal domin shiga zagaye na biyu

Gwamnatin Ghana ta tura dala miliyan uku a wani jirgi zuwa Brazil domin biyan 'yan wasan ladan ledar da suke takawa a gasar cin kofin duniya.

Mataimakin ministan wasanni Joseph Yamin ya shaida wa gidan rediyon Citi FM na kasar cewa: "'Yan wasan sun nace cewa suna son kudin ne a hannunsu.

"Sai da gwamnatin ta tattaro kudin sannan ta dauki hayar jirgi zuwa Brazil. Kudaden sun kai dalar Amurka miliyan uku."

Wajibi ne Ghana ta doke Portugal a ranar Alhamis idan har tana son samun damar tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

Karin bayani