Kocin Italiya zai yi murabus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sau hudu kasar Italiya na daukar kofin kwallon kafa na duniya.

Kocin Italiya Cesare Prandelli ya ce zai yi murabus bayan cire Italiyar a gasar cin kofin duniya na bana da ake gudanarwa a Brazil.

Wannan dai shi ne karo na biyu a jere da ake fitar da ita tun a zagayen farko daga gasar, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Uraguay inda suka tashi da ci 1-0.

Prandelli mai shekaru 56, ya karbi jagorancin kungiyar ta Azzuri bayan rashin nasarar da ta samu a gasar shekarar 2010, inda ya taimaka ta kai zagayen karshe a gasar Euro 2012.

Ya ce, "Na zabi wani salo don yin amfani da shi amma ban yi nasara ba, saboda haka na ga ya kamata na yi murabus."

Ya kuma kara da cewa, "Ban san mai ke faruwa ba, tun lokacin da aka sabunta kwantiragina al'amura suka sauya."