Kai tsaye: Nigeria da Argentina

Nigeria da Argentina Hakkin mallakar hoto Getty

Wannan shafi na kawo muku sharhi kai tsaye kan wasan Nigeria da Argentina da Iran da Bosnia a rukunin F na gasar cin kofin duniya. Latsa nan domin samun sabbin bayanai.

Mun kawo karshen sharhin da muke kawo muku kan wannan wasa amma za ku iya ci gaba da binmu a bbchausa.com domin samun cikakkun bayanai a kan gasar.

Ra'ayoyi daga Shafin BBC Hausa Facebook: Sarki Mai Madrid, Mu dai Super Eagles kun burge mu. Up Ahmed MUsa.

Hakkin mallakar hoto AFP

Nigeria ta tsallake zuwa zagaye na biyu inda za ta kara da France ko Ecuador

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An tashi wasa Argentina 3-2 Nigeria

Bosnia 3-1 Iran

Minti 87: Nigeria ta samu kwana ta hannun Garay amma Argentian sun fitar da kwallon ba tare da matsala ba.

Bosnia 2-1 Iran Idan aka tashi a haka Nigeria ce za ta tsallake

Minti 83 Argentina 3-2 Nigeria

Minti 80: Laevazzi ya yi laifi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Minti 79: Canji (Nigeria) Uche Nwofor ya karbi Peter Odemwingie.

Minti 78: Ahmed Musa ya kai kora amma Zabaleta ya hana shi yin tasiri

Minti 77: Argentina sun kai kora daga bugun tazara amma kwallo ta fita kwana amma an bugo ba wata matsala.

Minti 76: Onaze (Nigeria) ya janwo bugun tazara

Minti 74: Emenike (Nigeria) yayi satar gida.

Minti 73: Nigeria ta kai kora ta hannun Ahmed Musa amma kwallon ta yi sama tare da taimakon Peter Odemwingie.

Minti 70: Pablo Zabaleta (Argentina) ya yi laifi

Hakkin mallakar hoto Getty

Minti 68: Juwon Oshaniwa (Nigeria) ya jawo kwana amma kwalon ta fita ba tare da wata matsala ba.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Minti 66 Uchebo ya karbi Babatunde (Nigeria)
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Álvarez ya karbi Messi a minti na 63

Bosnia 2-0 Iran - Pjanic ya zira ta biyu a minti na 59

Minti 61: Nigeria ta kai mumunar kora ta hannun Mikel amma ya kasa buga kwallon sosai bayan an bugo kwana.

Minti 59: Messi ya kai kora amma kwallon ta fita sai dai ya yi korafin cewa an ture shi.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Minti 49 Kenneth Omeruo (Nigeria)

Hakkin mallakar hoto Getty
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Minti 49 Nigeria 2, Argentina 3. Marcos Rojo (Argentina) da kafar dama bayan an bugo kwana
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Minti 46 Nigeria 2, Argentina 2. Ahmed Musa (Nigeria) da kafar dama tare da taimakon Emmanuel Emenike.

An dawo hutun rabin lokaci zagaye na biyu

Sharhi: Alhaji Shehu Malami a BBC Hausa rediyo: Ya kamata Nigeria su gyara tsakiyarsu da kuma gefen dama na Ambrose. Ganin yadda Ángel Di María ke kai kora ta wurin.

Ra'ayoyi daga shafin BBC Hausa Facebook: Sanusi Muhammad Agentina sai ta yima Nigeria 3 da 1 insha Allahu sabilida juyayin harin bam din da ya faru da 'yan kasarmu Nigeria.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwallon da Ahmed Musa ya zira ita ce ta biyu na Nigeria ta ci a gasar
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Messi ya zira kwallaye hudu kenan kawo yanzu

Ra'ayoyi daga shafin BBC Hausa Facebook: Yusuf Raypower Gombe: Nigeria wasa na kyau, fatan zaku ci gaba da gashi.

An tafi hutun rabin lokaci Argetina 2-1 Nigeria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Argetina 2-1 Nigeria - Messi daga bugun tazara

Minti 45: Argentina ta samu bugun tazara bayan da aka tade Messi

Minti 43: Enyeama ya kai kwallo kwana bayan harin da Messi ya kai.

Minti 41: Onazi (Nigeria) ya kwanta bayan sun yi karo

Minti 38: Argentina ta kai kora ta kwana.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Minti 37: Lavezzi ya karbi Aguero

Minti 35: Nigeria ta samu bugun tazara a wuri mai kyau.

Minti 29: Argentina ta kai hari ta hannun Ángel Di María amma Enyeama ya ture kwallon waje.

Minti 26: Nigeria ta kai kora ta hannun Odemwingie amma kwallon bata yi tasiri ba tare da taimakon Efe Ambrose.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Bosnia 1-0 Iran - Dzeko 23′

Minti 24: Argentina sun kai kora ta hannun Di Maria amma Messi bai samu kwallo duk da cewa ya kwanta.

Sharhi: Aminu Abdulkadir a BBC Hausa rediyo: Ana zargin FIFA ko alkalan wasa na marawa manyan kasashe da 'yan wasansu baya.

Minti 22: Nigeria ta yi kokarin kai kora amma kwallo ta yi yawa ta fita ta hannun Emenike.

Minti 19: Argentina sun kai kora bayan kwallon da Messi ya bugu wacce Mikel ya sa kai.

Minti 18: Emenike ya fitar da kwallo amma yana korafin an ture shi. Argentina sun samu bugun tazara

Minti 16: Argentina sun samu kwana amma Enyeama ya cafke kwallon ba tare da matsala ba

Minti 13: Ángel Di María ya samu bugun tazara.

Minti 9: Sergio Agüero ya samu bugun tazara.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mintina 4: Argentina 1-1 Nigeria - Ahmed Musa ya narka kwallon a raga da kafar dama
Hakkin mallakar hoto AFP
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Minti biyu: Argentina 1-0 Nigeria - Messi ne ya dadata a raga bayan an kai hari ta dawo

Minti daya: An fara wasa

Sharhi: Alhaji Shehu Lawal a BBC Hausa rediyo: Kamata yayi 'yan Nigeria su mayar da hankali a kan 'yan gaban Argentina.

Iran ce kasa daya tilo da bata zira kwallo a gasar ta bana ba kawo yanzu.

16:55 An fara taken kasashen biyu inda aka fara da Nigeria

Sharhi: Ali Sadiq a BBC Hausa rediyo: Argentina na da kwararrun 'yan wasa kamata yayi Nigeria ta dage kada ta tsorata sosai.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Magoya bayan Argentina sun dau harami

16.50 Tawagar Argentina: Romero, Zabaleta, Federico Fernandez, Garay, Rojo, Gago, Mascherano, Di Maria, Messi, Higuain, Aguero.

16:44 Tawagar Nigeria: Koci Stephen Keshi ya fito da tawagar da doke Bosnia da ci 1-0 babu sauyi. Enyeama, Ambrose, Yobo, Omeruo, Oshaniwa, Onazi, Mikel, Babatunde, Odemwingie, Emenike, Musa.

16:39 Nigeria na bukatar maki guda domin ta kai zagaye na biyu, za kuma ta iya kai bantanta ko da an doke ta, matukar dai Iran ba ta yi nasara a kan Bosnia ba.

16.36 Za ku iya bayyana mana ra'ayoyinku kan yadda wasan ke gudana a shafukanmu na BBC Hausa Facebook da kuma Twitter.

16.30 Nigeria na bukatar maki guda domin ta kai zagaye na biyu, za kuma ta iya kai bantanta ko da an doke ta, matukar dai Iran ba ta yi nasara a kan Bosnia ba.