Nigeria ta kai zagaye na biyu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Messi ne ya zira kwallaye biyu

Nigeria ta tsallake zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya duk da ta sha kashi a hannun Argentina da ci 3-2.

Lionel Messi ya zira kwallaye biyu daga bangaren Argentina, yayin da Ahmed Musa ya zira biyu shi ma daga Nigeria.

Dan wasan na Barcelona ne ya fara zira kwallo a minti 3 da fara wa kafin Ahmed Musa ya rama bayan minti daya.

Messi ya kara ta biyu da bugun tazara daga yadi na 25 a minti na 45 sai dai Musa ya sake farkewa a minti na 47.

Sai dai Marcos Rojo ya zira kwallo ta uku a minti na 50 daga bugun kwana abinda ya baiwa Argentina damar lashe wasan.

Sakamakon ya nuna cewa Argentina ce te daya a rukunin na F da maki tara, yayin da Nigeria ta zamo ta biyu da maki hudu.

Bosnia-Hercegovina ta kasance ta uku bayan ta doke Iran da ci 3-1.

Karin bayani