Nigeria za ta fafata da Argentina

Hakkin mallakar hoto Getty

Dan wasan bayan Super Eagles, Godfrey Oboabona ya ce ya dawo daga jinyar raunin da ya ji a idon sawu, abin da ya sa bai buga wasan kungiyar da Bosnia-Hercegovina ba.

Sai dai ana ganin ba lallai ne Stephen Keshi ya sauya 'yan wasan da suka cinye Bosnia ba, yana iya yin barin Joseph Yobo, wanda zai buga wasansa na 100.

Argentina dai ta fito zuwa zagayen gaba, don haka kungiyar na iya hutar da wasu fitattun 'yan wasanta, sai dai dole ne ta doke Nijeriya idan tana son kasancewa kan gaba a rukunin F, kuma don ta kauce wa haduwa da Faransa mai tashen wasa.

Messi, wanda ya cika shekaru 27 ranar Talatar, shi ne kadai dan wasan da tauraronsa ke haskawa a cikin zakarun 'yan wasa hudu na Argentina a Brazil.

Super Eagles wadda karo uku a baya tana fuskantar Argentina a gasar kofin duniya amma ba ta taba nasara a kanta ba, a wannan karo tana bukatar yin kunnen doki don tsallaka wa zagaye na gaba, matukar Iran ba ta doke Bosnia a karawar da za su yi ba.