Ghana ta kori Muntari da Boateng

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun da farko an yi takaddama da 'yan wasa ka kudi

An kori Sulley Muntari da Kevin-Prince Boateng daga tawagar kwallon Ghana saboda zargin aikata rashin da'a.

Wata sanarwa da hukumar kwallon kafa ta Ghana ta fitar a shafinta na internet ta ce "an dakatar da 'yan wasan har illa ma sha Allah".

Boateng, na kulob din Schalke 04, an dakatar da shi ne "saboda gayawa kocin kasar Kwesi Appiah bakar magana a lokacin da suke horo a Maceio".

Shi kuwa Muntari an hukunta shi ne saboda abinda hukumar ta bayyana da "kai hari babu dalili ga daya daga cikin shugabannin hukumar kwallon kasar".

Hukumar ta kara da cewa lamarin na Muntari wanda ke taka leda a AC Milan ya faru ne a ranar Talata sannan aka bayyana Moses Armah, a matsayin jami'in da dan wasan ya ci zarafi.

Labarin na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnatin kasar ta tura dala miliyan uku zuwa Brazil domin biyan 'yan wasan kudin garabasarsu.

Karin bayani