An fitar da Ghana da Portugal

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ghana, Ivory Coast da Kamaru duka sun koma gida

Cristiano Ronaldo ya zira kwallo a karon farko a gasar cin kofin duniya ta bana a wasan da Portugal ta doke Ghana da ci 2-1, sai dai duka kasashen sun fice daga gasar.

Dan bayan Ghana ne John Boye ne ya ci kansu, sai dai Asamoah Gyan ya farke wa Ghana da ka.

Ronaldo ne ya zira wa Portugal kwallo ta biyu bayan da golan Ghana Dauda ya yi kuskure wajen fitar da kwallo - abinda ya baiwa Portugal dama.

Sai dai basu iya zira kwallaye ukun da suke bukata ba domin tsallake wa, abinda ya baiwa Amurka dama saboda ta fi su yawan kwallaye.

Amurka ta sha kayi a hannun Jamus da ci 1-0 a daya wasan na rukunin.

Karin bayani