"Tsare matar Hamma bita da kulli ne"

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Rahotanni sun ce baya ga Najeriya, ana safarar jarirai daga wasu kasashen yammacin Afirka.

A Jamhuriyar Niger, lauyan iyalan shugaban majalisar dokokin kasar Barista, Sule Umaru ya ce, tsare mai dakin Hamma Amadun, Hajiya Hadiza a gidan kaso bita da kullin siyasa ne.

A cewarsa, hukumomin kasar ba su da kwararan hujjojin da ke tabbatar da zargin da su ke yi wa mai dakin ta shugaban majalisar dokokin.

Lauyan iyalin na Hama Amadu ya fadi hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya kira a Yamai a ranar Alhamis.

Ana dai zargin matar shugaban Majalisar dokokin ne tare da wasu mata da laifin sayo jarirai daga Najeriya.