Manchester United sun sayi Herrera

Hakkin mallakar hoto
Image caption Herrera ne dan wasan farko da United ta saya a kakar bana

Manchester United sun tabbatar da sayen dan wasan tsakiya Ander Herrera daga Athletic Bilbao.

Kulob din na La Liga sun yi watsi da tayin fan miliyan 29 daga United kan dan wasan na Spain a safiyar ranar Alhamis.

Sai dai Herrera ya sauya daya daga cikin sharudan kwantiraginsa wacce ta sa ya zamo dan wasa na farko da United ta saya karkashin Louis van Gaal.

"Koma wa Manchester United abu ne da na dade ina mafarki," a cewar Herrera, wanda ya amince ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru hudu.

"Na komo United ne domin tallafa wa kulob din ya cimma dukkan abinda suka sanya a gaba.

Karin bayani