Hukuncin Suarez ya yi tsauri - Chiellini

Giorgio Chiellini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jama'a da dama sun soki Luis Suarez kan lamarin

Dan wasan Italy Giorgio Chiellini ya ce hukuncin dakatarwar watanni hudu da aka yanke wa Luis Suarez saboda cizonsa ya yi tsauri.

Suarez, mai shekaru 27, ya ciji dan wasan na Juventus ne lokacin da Uruguay ta doke Italy da ci 1-0, kuma an dakar da shi daga dukkan al'amuran kwallon kafa na watanni hudu.

Chiellini, ya ce "bai ji dadi ba", kuma ba ya tunanin ramuwa ko jin haushin Suarez".

Suarez ya kuma samu goyon bayan shararren tsohon dan kwallon duniya wanda ya taba lashe gasar cin kofin duniya Diego Maradona, wanda ya ce tsaurin hukuncin abin kunya ne.

Karin bayani