Jonathan ya baiwa S Eagles tabbaci

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Super Eagles za su kara da Faransa a zagaye na biyu

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya baiwa manyan 'yan wasan kasar tabbacin cewa za a biya su kudaden garabasarsu na gasar cin kofin duniya.

Tabbacin shugaban kasar ya zo kwana guda bayan da 'yan Super Eagles suka ki halartar horo ranar Alhamis.

BBC ta fahimci cewa 'yan wasan Nigeria na jin tsoron cewa ba za a biya su ba idan gasar ta kare - lamarin da ya faru bayan gasar cin kofin nahiyoyi.

Nigeria za ta kara da Faransa ranar Litinin a zagayen 'yan 16 bayan da suka zo na biyu a rukunin F.

A yayin da 'yan wasan ke bukatar kudinsu nan take, ita kuwa hukumar kula da kwallon Nigeria (NFF) cewa take, ba za ta iya biya ba sai ta karbi kudadenta daga hannun hukumar kwallon duniya Fifa.

Hakan ne kuma ya sa shugaba Jonathan ya shiga tsakani. Akwai tantama kuma kan adadin kudaden da 'yan wasan ke bi.

BBC ta fahimci cewa 'yan wasan na ganin an rage musu dala 15,000 kowannensu kan abinda ya kamata su samu saboda kaiwa zagaye na biyu.

Karin bayani