'Yan Super Eagles na rikici kan kudi

Image caption Super Eagles za su kara da Faransa a zagaye na biyu

Tawagar Super Eagles ta Nigeria sun ki halartar horon da aka shirya za su yi saboda rikici kan kudaden da za a biya su (bonus).

'Yan wasan na bukatar a biya su kudaden garabarsar da aka yi musu alkawari idan suka tsallake zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya.

An shirya za su yi horo a Campinas ranar Alhamis sai dai basu shiga motar da ya kamata ta dauke su ba saboda suna tattaunawa. Daga baya jami'ai sun tabbatar cewa an soke horon.

Nigeria za ta kara da Faransa ranar Litinin a zagaye na biyu bayan da suka zo na biyu a rukunin F.

Sai dai babu tabbas ko za su tafi zuwa Brasilia kamar yadda aka tsara.

Ba wannan ne karon farko da Super Eagles suka dauki mataki irin wannan kan kudi ba - a bara sun halarci gasar cin kofin zakarun nahiyoyi a makare.

Karin bayani