Luke Shaw ya koma Manchester United

Luke Shaw Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luke Shaw na daga cikin matasan 'yan wasan Ingila

Dan wasan baya na Southampton da Ingila Luke Shaw ya koma Manchester United a kan kudi fan miliyan 27, wanda ka iya kaiwa miliyan 31 gwargwadon nasarar da yayi.

Tun da farko United ta taya dan wasan ne mai shekaru 18 fan miliyan 27 a watan Mayu, amma aka yi watsi da tayin.

Shaw ya shaida wa Southampton cewa yana son koma wa United a karshen kakar wasannin da ta gabata.

Ya zamo dan wasan farko mafi kankantar shekaru da ya taka leda a gasar cin kofin duniya ta 2014 bayan da ya buga minti 90 a wasan Ingila da Costa Rica ranar Talata.

Shi ne dan wasa na biyu da United ta saya a kakar bana - kuma na biyu a 'yan kwanaki - bayan da suka sayi dan Spain Ander Herrera daga Athletic Bilbao a kan fan miliyan 29.

Karin bayani