Colombia ta fitar da Uruguay da ci 2-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Colombia za ta kara da Brazil a wasan dab da na kusa da karshe a mako mai zuwa

Colombia ta kai wasan dab da na kusa da karshe a gasar cin kofin duniya da ake yi a Brazil bayan ta doke Uruguay da ci 2-0.

Kwallayen da James Rodriguez ya ci a minti na 28 da kuma minti na 50 su suka ba wa kasar damar bin sahun Brazil zuwa matakin na gaba.

Kwallaye biyar ke nan James Rodriguez ya ci a gasar ta kofin duniya da ake yi a Brazil.

Kafin wannan wasan, Brazil ce ta fara tsallake wa zuwa wannan mataki bayan ta fitar da Ruguay a bugun fanareti da ci 4-3.

Karin bayani