Luke Shaw zai koma Manchester United

Mai tsaron gida na kungiyar kwallon kafa ta Southhampton Luke Shaw zai koma taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sayi dan wasan kwallon kafa akan kudi fam miliyan 27,abin da kuma ya sa ya zamo daya daga cikin matasa da za a cepanar akan kudi masu dimbim yawa.

Mataimakin mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na Manchester United, Ryan Giggs ya ce dan wasan ya sa hanu akan kwantaragi taka leda a kungiyar har na tsawon shekara hudu.

Luke Shaw shi ne dan wasa me kankanci shekaru da ya buga kwallo a gasar kwallon kafa ta FIFA dake gudana a Brazil kuma ya yi wasa lokacinda Ingila ta kara da Costa Rica inda suka yi kunen doki.