Brazil 2014: Costa Rica da Girka

'Yan wasan Costa Rica Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Costa Rica ta lallasa manyan twagogin kwallon kafa kafin ta kai wannan matakin

Mutane kalilan ne za su yarda idan aka ce musu Costa Rica za ta iya lallasa Ingila, da Italiya da Uruguay, ta kuma dare saman rukunin D a Gasar Cin Kofin Duniya a Brazil.

Hakazalika, mutane da dama sun yi zaton da kyar Girka ta kai labari; sai ga shi tawagogin biyu sun ba da mamaki, sun tsallaka zagaye na 'yan 16 za kuma su fuskanci juna.

Ana dai sa ran Costa Rica za ta yi amfani da 'yan wasanta wadanda suka lallasa Italiya a wasansu na biyu a rukunin da suke, yayin da kyaftin din Girka Kostas Katsouranis zai shiga fili bayan da, sakamakon dakatar da shi da aka yi, bai buga wasansu da Ivory Coast ba.

Kocin Girka, Fernando Santos, ya ce: "Wajibi ne mu yi taka-tsantsan sosai a wannan wasan, saboda Costa Rica ce ta kasance a saman 'Rukunin Mutuwa'. Saboda haka ba za mu yi musu da wasa ba".

Karin bayani