A binciki rawar Ghana —Mahama

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tuni tawagar Ghana ta koma gida bayan fitar da ita daga Brazil 2014

Shugaba John Mahama na Ghana ya bukaci a gudanar da bincike a kan faduwar bakar tasar da tawagar kasar ta yi a Gasar Cin Kofin Duniya da ake bugawa a Brazil.

Tawagar kasar ta Ghana dai ta kare da maki guda ne kacal a rukunin G na gasar, wanda ta samu sakamakon canjaras din da ta yi, 2-2, da Jamus.

Wata takaddama ta kuma barke a tawagar dangane da biyan kudin 'yan wasa ranar Larabar da ta gabata, Ranar Alhamis kuma aka kori 'yan wasan tsakiya Sulley Muntari da Kevin-Prince Boateng bisa zargin rashin da'a.

Jiya Lahadi ne dai 'yan wasan na Ghana suka sauka a Accra, babban birnin kasar; kyaftin dinsu Asamoah Gyan na cikin jirgin saman da ya mayar da 'yan wasa da jami'an Black Stars din gida.

Karin bayani