Brazil 2014: Holland ta sallami Mexico

Wasan Holland da Mexico Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Bayan Mexico ta fara samun nasara, a karshe Holland ta kora ta gida

A daya daga cikin wasannin zagayen 'yan 16 na Gasar Cin Kofin Duniya da ake bugawa a Brazil, ranar Lahadi Holland ta dakile yunkurin Mexico na kaiwa quarter finals da ci biyu da daya.

Har lokacin da aka tafi hutun rabin lokaci dai, babu wanda ya jefa kwallo a cikin tawagogin biyu.

Sai dai kuma labarin ya sauya minti uku bayan dawowa daga hutun rabin lokaci lokacin da Giovani dos Santos ya ciyo wa Mexico kwallonta, al'amarin da ya sa ta fara hango alamun nasara a wasan, musamman ganin irin sakacin da 'yan wasan Holland suka rika yi.

Sai dai ana minti na arba'in da uku na rabin lokaci na biyu, Wesley Sneijder ya farke wa Holland bayan da ya dirka kwallonta ta farko a ragar Mexico.

Bayan nan ne Arjen Robben ya fadi kasa a bakin ragar Mexico; alkalin wasa kuma ya baiwa 'yan wasan Holland bugun fanariti a daidai minti na biyu na karin lokaci.

A minti na hudu na karin lokacin Klaas-Jan Huntelaar ya kawo karshen fatan Mexico bayan da ya ciyo wa Holland kwallonta ta biyu da bugun na fanareti.

Karin bayani