"Ya kamata Liverpool ta rike Suarez"

Luis Suarez Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption FIFA ta dakatar da Luis Suarez ne saboda ya gantsarawa wani dan wasa cizo

Wani tsohon darakta a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Damien Comolli, ya shawarci kungiyar ta rike Luis Suarez hannu bibbiyu duk kuwa da dakatar da shi da aka yi.

Mista Comolli ne ya taimaka kungiyar ta dauki dan wasan a shekarar 2011.

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, wato FIFA, ce ta dakatar da dan wasan gaban dan kasar Uruguay daga duk wani wasa har tsawon watanni hudu bayan da ya gantsara wa dan wasan Italiya, Girgio Chiellini, cizo yayin wani wasa a Gasar Cin Kofin Duniya.

Wannan ne dai karo na uku a rayuwarsa ta kwallon kafa da aka dakatar da Suarez saboda ya gantsarawa wani cizo; karo na biyu kuma tun bayan da ya fara buga wasa a Liverpool.

Barcelona ta nuna sha'awarta ta sayen Suarez, amma Comolli ya ce lallai kamata ya yi Liverpool ta ci gaba da rike shi.

Dakatarwar ta FIFA dai na nufin Suarez ba zai shiga filin wasan kwallon kafa ba, kuma ba dama ya yi atisaye da kungiyarsa ko da tawagar kasarsa.

Karin bayani