Batun azumi ya fusata kocin Algeria

Vahid Halilhodzic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shi kansa kocin na Algeria Vahid Halilhodzic Musulmi ne

Kocin Algeria Vahid Halilhodzic ya ki yin magana kan 'yan wasan da ke yin azumi a cikin tawagar da wadanda ba sa yi a lokacin da suke shirin tunkar Jamus a gasar cin kofin duniya.

An fara azumin ne ranar Lahadi kuma Halilhodzic, mai shekaru 61, ya nuna bacin rai kan tambayoyin da aka rinka yi masa a lokacin da yake taron manema labarai.

"Wannan lamari ne na sirri kuma idan aka yi tambaya a kansa to ka nuna rashin girmamawa da daraja," a cewar kocin dan Bosnia.

"Yan wasan suna da zabi su yi abinda suka ga dama kuma muna so mu kawo karshen wannan takaddamar."

Azumin Ramadan wajibi ne ga dukkan al'ummar Musulmai kuma yana daya daga cikin rukunan Musulunci, duk da cewa an daukewa wadanda basu da lafiya, mata masu juna biyu da tsofaffi.

Karin bayani