Murray ya yi nasara kan Anderson

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Andy Murray ya taka rawar gani sosai a wasan

Mai rike da kanbun gasar tennis ta Wimbledon Andy Murray ya doke Kevin Anderson na Afrika ta Kudu domin kaiwa zagayen dab da na kusa da na karshe a karo na bakwai a jere.

Murray ya yi nasara da ci 6-4 6-3 7-6 (8-6) a wasan da har sai da aka rufe filin saboda ruwan sama.

Dan wasan na Burtaniya zai kara da zakaran Queen Club Grigor Dimitrov a zagaye na gaba.

Murray, mai shekaru 27, a yanzu ya lashe wasanni 17 a jere a filin All England Club, tun daga gasar Olympic ta London 2012.

Yana kan hanyarsa ta rike kanbunsa na Wimbledon domin cimma Fred Perry, dan Burtaniya na karshe da yayi haka a shekarar 1936.

Karin bayani