Za a iya hukunta Arjen Robben

Arjen Robben Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fanaretin da Robben ya samo ne ya baiwa Holland damar doke Mexico

Dan wasan Netherlands Arjen Robben zai iya fuskantar hukunci daga hukumar kwallon kafa ta duniya bayan da ya bayyana cewa ya yi langwai a wasansu da Mexico.

Dan wasan mai shekaru 30 ya ce bai yi langwai ba wurin samun bugun fanareti a karin lokaci na wasan ba, sai dai ya shaida wa gidan talabijin na kasarsa: "Ina neman afuwa. Na yi langwai a zagayen farko."

Kocin Mexico Miguel Herrera wanda ya fusata ya zargi Robben da yin langwai har sau uku a lokacin wasan.

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya Fifa, ta ce za ta iya "hukunta wadanda suka sabawa dokokinta".

Sai dai mai magana da yawun Hukumar ta Fifa Delia Fischer, ta ce "ba ta da masaniya kan cewa za a hukunta dan wasan".

Sashi na 57 na dokokin Fifa za su yi aiki ne bayan da Robben ya amsa cewa yayi langwai.

Haka kuma sashin na 77 na dokokin ya baiwa kwamitin ladaftarwa na hukumar ikon "daukar mataki kan manyan laifukan da alkalin wasa bai gani ba da kuma goge kuskuren da alkalin wasa ya yi".

Fanaretin da Robben ya samo ne ya baiwa Holland damar doke Mexico.

Karin bayani