Keshi ya musanta yin murabus

Stephen Keshi Hakkin mallakar hoto google
Image caption An nada Stephen Keshi ne a matsayin kocin Nigeria a shekarar 2011

Kociyan Nigeria, Stephen Keshi ya musanta cewa ya yi murabus bayan da aka yi waje da Nigeria daga wasan cin kofin duniya a Brazil.

Stephen Keshi ya ce ba a fahimci bayanan da ya yi ba a lokacin da ya ke jawabi ga 'yan wasan Super Eagles bayan kammala wasansu da kasar Faransa inda Nigeria ta sha ka shi da ci 2-0.

"Abin da na ce shi ne mai yiwuwa wannan shi ne wasa na karshe da zan jagoranta a matsayin mai horas da 'yan wasan Super Eagles saboda kwantiragina ya kawo karshe ne bayan kammala gasar cin kofin duniya kuma kawo yanzu ba'a sabunta kwantiragin ba."

A baya dai Stephen Keshi ya taba mika takardar yin murabus din sa bayan da Nigeria ta lashe kofin nahiyar Afrika, inda ya bayyana rashin samun goyan baya da kuma karramashi.

Amma daga bisani ministan harkokin wasanni na lokacin ya shawo kansa ya ci gaba da aiki.