Diego Costa ya koma Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Costa ya taimaki Atletico ta lashe gasar La Liga

Chelsea ta tabbatar da kamalla cinikin dan kwallon Spain, Diego Costa daga Atletico Madrid.

Dan wasan mai shekaru 25 tun kafin a soma gasar cin kofin duniya ake cinikin komawarsa Stamford Bridge.

Wata sanarwa daga Chelsea ta ce an kamalla yarjejeniyar musayar dan kwallon tare da Atletico Madrid.

Diego Costa ya haskaka a kakar wasan da ta wuce a gasar La Liga ta Spain inda ya zura kwallaye 27 ya taimaki kungiyar ta lashe gasar La Liga ta bana.

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya dade yana kukan cewar yana bukatar dan wasan gaba mai kyau wanda ya kware a wajen fasa raga.