Chelsea ta sallami Cole da Eto'o

Samuel Eto'o Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shekara guda kawai Samuel Eto'o ya yi a Chelsea

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta saki tsohon dan kwallon Ingila Ashley Cole da dan Kamaru Samuel Eto'o.

Kwantiragin 'yan wasan biyu, dukanninsu masu shekaru 33, ya kare ne a ranar Litinin, kuma babu wanda aka sabunta wa.

"Cole zai iya kasancewa dan wasan da ya fi kowanne a tarihin kulob din a bangaren da yake bugawa," a cewar sanarwar da kulob din ya fitar.

"Chelsea sun gode wa Ashley saboda gudummawar da ya bayar a shekaru takwas din da ya shafe da kuma taimakawa wurin lashe kofuna da dama."

Eto'o ya bar kulob din ne bayan ya zira kwallaye 12 a wasanni 35 bayan da ya sanya hannu kan kwantiragin shekara guda daga kungiyar Anzhi Makhachkala ta Rasha a bara.

Karin bayani