Wimbledon: An fitar da Andy Murray

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rabon da a fitar da Murray a wannan mataki tun 2008

Dan Bulgaria Grigor Dimitrov ya fitar da mai rike da kanbun gasar Wimbledon Andy Murray daga gasar a zagayen dab da na kusa da na karshe.

Dimitrov, mai shekaru 23, ya taka rawar gani sosai inda ya lashe wasan da ci 6-1 7-6 (7-4) 6-2 a sa'o'i biyu da minti daya inda ya tsallake zuwa wasan kusa da na karshe a karon farko.

Murray ya shafe wasanni 17 ba a yi galaba a kansa ba a Wimbledon kuma yana kokarin kaiwa wasan kusa da na karshe ne a karo na shida a jere.

Wannan ne karon farko tun shekara ta 2008 da ya kasa kaiwa zagayen kusa da na karshe.

Dimitrov, ya shige gaban Murray a kusan dukkan fannonin wasan, wanda ya rinka yin kuskure a lokuta daban-daban.

Karin bayani